GAYYATA ZUWA GA BIKIN NADI SARAUTA TAFAKIN LAKWAJA, INJINI ABDULSALAM

BY THEANALYSTMEDIA.

Iyalan Marigayi Alhaji Abdulsalam Bila na unguwar Madabo Lakwaja, suna gayyatar jama’a zuwa wurin bikin rawani na dansu Alhaji Injiniya,Sagir Abdulsalam Bila, TAFAKIN LAKWAJA (DAUDU),Wanda mai martaba Sarkin Lakwaja ,Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, Maigarin lakwaja kuma shugaban majalisar sarakunan karamar hukumar Lakwaja, wanda aka tsara kamar haka:

Bikin nadin sarauta : RANAR 13 GA SATUMBA, 2025.

Wuri: FADAR MAI MARTABA MAIGARI.

LOKACI: 9 na safe.

Wurin LIYAF : UNGUWAR MADABO , LAKWAJA.

Allah ya albarkace ku baki daya yayin da kuke girmama gayyatarmu, tare da yi muku fatan alheri cikin shiriyar Allah da kariyarsa. Ameen.

Sa hannun : Kwamitin Shirya, KAFEKIN NA LOKOJA.

Visited 7 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  Maigarin Lakwaja Ya Bawa Ali Abubakar Tanko Ali Sarautar Gargajiya na "SHAMAKIN LAKWAJA"