Dan Malikin Lakwaja Ya Taya Baba’ango murna A Matsayin Amirul Hajj.2025

Daga Musa Tanimu

Alhaji Baba’ango Idris

Malikin Lakwaja, Alhaji Danladi Abdulsalam ya taya Sakataren Majalisar Malamai na Jihar Kogi kuma tsohon Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kogi, Alhaji Baba’ango Idris murnar nadin da Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya yi masa a matsayin Amirul Hajj.2025.

Sakon na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dan Maliki a ranar Talata kuma ya mikawa jaridar TheEANLYSTNG dake Lakwaja cewa nadin tsohon sakataren zartarwa ya samo asali ne daga irin kwazonsa, jajircewa da rikon amana.

“Ina da kwarin gwiwa da kuma fatan Alhaji Baba’ango Idris zai kawo arziƙin iliminsa da gogewarsa wajen gudanar da wannan gagarumin aiki”. Yace.

See also  Kungiyar tuntuba ta dattawan Lakwaja (LECFOR) ta kai ziyarar ban girma ga shugaban jam'iyyar APC Baba Ali

Abdulsalam ya kuma yi kira ga Amirul Hajj 2025 da ya ba da hujjar amincewar da gwamnatin jihar Kogi ta yi masa na ganin ya yi aikin hajjin 2025 zuwa Saudiyya cikin nasara ba tare da cikas ba.

Ya yi masa addu’ar samun nasara da kuma shiriyar Allah wajen gudanar da aikin da aka dora masa.

Visited 24 times, 1 visit(s) today
Share Now