Matar Sheikh Nayashi, Sayyida Hauwa’u Ta Rasu

Daga Wakilinmu

Allah ya yiwa Hajiya (Sayyida) Hauwa’u Sheikh Tanko Nayashi rasuwa, babbar diyar marigayi Sheikh Yusuf Abdallah Ellokojiy

Sayyida Hauwa’u ta rasu ne a daren Asabar bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Inusa Nayashi ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hauwa’u a makabartar iyali da ke cibiyar koyar da harshen Larabci da Musulunci ( Markaz) Lakwaja da karfe 11 na safiyar Lahadi.

Marigayi ta rasu ta bar mijinta, Sheikh Tanko Nayashi, ‘yan uwanta sun hada da, Khalifa Nurudeen Yusuf Abdullah, Nasir Yusuf Abdullah, Siraj Yusuf Abdullah da Ibrahim Nyass Yusuf Abdullah.

Sayyida ta kuma bar ‘ya’ya Wanda ya hada da: ustaz Mansur Nayashi,Maitawali’u Nayashi da Inusa Nayashi.

See also  GOVERNOR BELLO, PRINCE SHUAIBU ABUBAKAR AUDU, APC NATIONAL CHAIRMAN, OTHERS PRESENT AS PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU HANDS OVER FLAG OF VICTORY TO APC'S ODODO AT PRESIDENTIAL VILLA

Allah ya jikanta da rahamar sa, Ya gafarta mata dukkan kurakuranta, ya baiwa iyalai karfin gwuiwa da su juyar da batacce, amin.

Visited 4 times, 4 visit(s) today
Share Now

Leave a Reply