Daga Musa Tanimu Nasidi
Dan Darman Lakwaja, Barista Nasir Ahmed, ya taya Maigarin Lakwaja kuma shugaban majalisa Sarakunan karamar hukumar Lakwaja, maimaita Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, murnar cika shekaru 1 da hawansa karagar mulki.
Barista Ahmed, a cikin wata sanarwa da ya fitar da kan sa ya bayyana cewa shi da iyalan marigayi Sarkin Yakin Lakwaja, Alhaji Muhammad Karaworo Ahmed sun yi farin ciki da yadda Maigari ya rayu domin shaida bikin cika shekara daya na sarauta a kan karagar manyan magabatansa.
Ya bayyana Sarkin a matsayin fitaccen mai gudanar da mulki, fitaccen dan jiha kuma jagora abin koyi wanda mulkinsa ke wakiltar wani muhimmin al’amari a tarihin Masarautar Lakwaja da Jihar Kogi baki daya.
Da yake bayyana Alhaji Ibrahim Gambo Kabir a matsayin uba ga kowa da kowa, Dan Darman Lakwaja ya jinjinawa Maigari bisa ga irin gudunmawar da ya bayar wajen hadin kai da hakuri kafin da bayan nadin sarautar.
Jigon Dan kasuwa kuma Baban Lauyan ya yaba wa sarki da nagartattun mutanen masarautar Lakwaja bisa goyon bayan da suke baiwa mai martaba Maigari, kuma
yayi masa fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka da lafiya.