
Daga Wakilinmu
Yayin da kungiyar matan Lakwaja (Allah Naso) ke gudanar da Maulidi a duk shekara, Shugaban karamar hukumar Lakwaja, Kwamared Abdullahi Adamu ya bukaci musulmi da su yi koyi da Annabi Muhammadu tare da samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummarsu da karma hukuma baki daya.
Adamu, ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin a wajen taron Maulidin na bana wanda Hajiya Fatima Marka Yahaya Abbas ta shirya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmin jihar da ma sauran su da su yi amfani da wannan biki na tunawa da maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad, domin samar da zaman lafiya da hadin kai.
A yayin da yake mika sakon taya murna ga shugabar kungiyar Hajiya Fatima Marka Yahaya Abbas, Adamu ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa karma hukuma Lakwaja da jihar addu’ar zaman lafiya.
A nasa jawabin kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kogi, Injiniya Muhammad Danladi Yahaya Farouk, ya yi kira ga al’ummar musulmi da su yi amfani da ruhin Maulidi wajen nuna kishin kasa, soyayya da zaman lafiya.
Farouk ya jaddada cewa bukin maulidin Annabi Muhammad lokaci ne da ya dace mu rungumi ka’idojin kyakkyawar makwabtaka da zama masu kula da ‘yan uwanmu.
Tun da farko, babban limamin masallacin Kutepa, Sheikh Abu-Bila, ya ce Idin Maulidi lokaci ne na tunani kan koyarwar Manzon Allah na hadin kai da tausayi da zaman lafiya.
Hajiya Fatima Marka Yahaya Abbas a wata tattaunawa da ta yi da kafar yada labarai ta THEANLYSTNG, ta bayyana jin dadin ta ga daukacin manyan baki da suka halarci bikin tare da yi musu addu’ar Allah ya kai su gidajen su lafiya.
Maulidin na bana ya samu halartar Wazirin Lakwaja, Alhaji Abdulrahman Idris Baba kurum, Wanda ya wakil ce mai martaba Sarkin Lakwaja Shatiman Lakwaja, Alhaji Muhammad mabo Kasim, shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Maikudi Bature da sakataren karamar hukumar Lakwwaja, Abubakar danjuma Muhammad.
Sauran sun hada da: tsohuwa DLG, karamar hukumar Lakwaja, Hajiya Fati Abubakar angulu agaba, masu rike da mukaman gargajiya da malaman addinin musulunci da dama.

