Injiniya Farouk, Shatima na Lakwaja, Wasu Sun Halarci Marigayi Maigari Daurin Auren Diyar Marigayi Maigarin Lakwaja

Daga Musa Tanimu Nasidi

Hayar zuwa fadar mai martaba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, a ranar Juma’a, ya samu fitowar jama’a da dama yayin da Maimunat Kabir Maikarfi ‘yar marigayi Maigarin Lakwaja ta daura aure da masoyinta, Dr Abdulazeez Muhammad, ma’aikacin asibitin koyarwa na jami’ar taraya na Lakwaja.

An gudanar da bikin ne a fadar Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, wanda babban limamin Lakwaja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban ya jagoranta, wanda ya samu taimakon malaman addinin musulunci na ciki da wajen jihar Lakwaja.

Hakimin Cikin Gida, Alhaji Tale Abbas ya wakilci mahaifin amaryar (HRH Maigarin Lakwaja ) inda aka biya sadakin Naira 100,000 wanda Wakilin angon, Alhaji Abdulazeez sani ya bayar.

See also  Hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba: Shugaban kwamitin riko na Lakwaja ya gana da masu ruwa da tsaki

Daga cikin fitattun mutanen da suka halarci taron sun hada da, kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kogi, Injiniya Muhammad Danladi Yahaya Farouk, Shatiman Lakwaja, Alhaji Muhammad Mabo Kasim, wakilan khalifa Nurudeen Yusuf, sarakunan gargajiya, masu rike da sarautar gargajiya da dai sauran su.

Da yake zantawa da manema labarai, kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kogi ,Injiniya Farouk, yayin da yake taya ma’auratan da iyayensu murna, ya bayyana cewa aure a matsayin cibiyar yana bukatar amincewa da fahimtar juna, inda ya bukaci amarya da angonta da su mutunta juna tare da bin koyarwar addinin musulunci. aurensu.

Visited 4 times, 2 visit(s) today
Share Now

Leave a Reply