Eid-al-Fitr: Cigarin Lakwaja ya taya al’ummar Musulmi murna, ya kuma bukaci a kara addu’o’in samun zaman lafiya.

Daga Aliyu Abdulwahid

Cigarin Lakwaja,Alhaji Ahmed Sanusi ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar azumin watan Ramadana da aka shafe kwanaki 30 ana yi, sannan ya bukaci addu’o’in samun zaman lafiya a Masarautar Lokoja, jihar Kogi da Najeriya baki daya.

Wata sanarwa da da kan sa ya sanya wa hannu a ranar Laraba a Lokoja ta ce, watan Ramadan ya ba da damar yin addu’a da neman taimakon Allah kan matsalar tsaron kasar nan.

Sanarwar ta kara da cewa, ya kamata al’ummar musulmi su ci gaba da aiwatar da darussan da suka koya a cikin watan Ramadan ko da bayan watan ya kare.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Eid-al-Fitr wani lokaci ne na farin ciki mai girma domin yana nuna nasarar kammala azumi da kuma tunani na ruhaniya a cikin watan Ramadan mai alfarma.

See also  I’m not like Yahaya Bello, Says Wike

“A ranar Idi, musulmai suna nuna godiya ga lafiya da damar da Allah ya basu na sauke nauyin da aka dora musu na azumi.

“Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin biki don inganta zaman lafiya da juna.

“Ina taya Maigari na Lokoja murna ga daukacin al’ummar musulmi da masu rike da sarautar gargajiya na Lokoja, Allah ya kara mana bukukuwan ibada” Cigari ya yi addu’a.

Visited 13 times, 1 visit(s) today
Share Now