Al’ummar Ward D sun kama Wanda ake zargin Sata, an mika shi ga ‘yan banga na Jiha

Daga Alfaki Nasidi

Wani matashi dan shekara 33 mai suna Hassan Salihu, ya shiga hannun jami’an hukumar ‘yan banga ta jihar Kogi da ke karamar hukumar Lakwaja bisa zarginsa da satar kayan lantarki na dubban Naira a unguwan Kura, ward D, karamar hukumar Lakwaja ta jihar Kogi.

JaridaManazarcin ya tattaro cewa wanda ake zargin wanda ke zaune a unguwar kwakwa Tophill, unguwan Kura Street, Lakwaja, wasu matasan unguwar ne suka kama shi ga jami’in ‘yan banga Muhammed Ghadafi da ke aiki da ‘yan banga na jihar Kogi.

Aminu Hassan da wasu mutane uku da ake zargin yanzu haka, ana zargin su ne masu sayen kadarorin da aka sace.

See also  FULL LIST: 42 microfinance banks lose licences

Da yake tabbatar da kamun, Hakimi na ward D, Isah Baba Nasidi, ya ce wanda ake zargin dan kungiyar asiri ne da ke addabar al’umma.

“Muna so mu yi kira ga jama’a da su lura sosai idan mutane suka zo suna son yin haya a gidanku, yawanci sai su yi sata kamar Salihu wanda ya shafe watanni uku a cikin al’umma yana gudanar da ayyuka sama da gidaje uku,” in ji Nasidi.

Visited 4 times, 1 visit(s) today
Share Now