Daga Musa Tanimu Nasidi
Awuzu billahi mina shaidani rajim bisminlah rahamani Raheem.
Assalamu Alaikum jamma’ah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai da ya bamu aron lokaci ya kuma tara mu a wanna wuri mai tarin albarka.
Sallati da yabo kun fiyayyen halita Manzon Rahama Sayyadina Muhammadu SAW.
Bayan haka
Godiya da jinjina ma mai girma Gwauna jahar kogi, Alhaji Yahaya Bello na tabbabta da ni Maigarin lakwaja Allah ya saka masa da alkhairi duniya da lahira. Ameen
Inna Kara gode ma wayanda Allah ya aza masu nauyi zaben sarki wato (Kingmakers) nayin abinda ya dace. Allah ya saka masu da alkhairi.
Ina Mika ta’azi zuwa ga zurian sarki bukar Allah na farko Allah ya gafarta masa. Sarki Dauda Allah ya gafarta masa. Sai Kakanina Sarki Muhammadu maikarfi na farko, Sarki Yahaya Muhammadu Maikarfi, Sarki Muhammadu Kabiru Allah ya jikansu gaba dayan suw Aameen.
Godiya ta musamma ga jamma’ah garin lakwaja akan soyayya da kaunan da suka nuna mana tun farkon tafiya har lokacin da Allah ya tabbatar da ni Maigarin Lakwaja Allah ya saka masu da alkhairi.
Inna amfani da wanna dama niman afuwan duk wayanda suka tunanin nayi masu ba daidai ba saboda ni na yafe wa kowa bani da makiya kowa masoya na ne.
Inna kira ga jamma’ah da muhada kai saboda haka shine zai kawo mana alkhairi a gari.
Inna rokon matasan mu da muguje ma abinda zai kawo tashin hankali a gari.
Inna rokon Iyayen mu musanya idanuwan mu akan yaran mu kuma, Mu nemi ilmi Addini da na boko kuma muyi Sana’a.
Allah ya jikan iyayen wayan da suka yi wafati.
Sallamu alaikum.