Cigarin Lakwaja, tsohon dan majalisa, ma’aikatan NIWA Wasu sun halarci bikin auren Barista Dadadu

Daga Musa Tanimu Nasidi

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma Cigari na Lokoja, Alhaji Ahmed Muhammad Sanusi, tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Lokoja 1, Hon Isah Tanimu Umar, sakataren majalisar malamai na jihar Kogi, Alhaji Baba’ango Idris, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt. Hon. Umar Imam da manyan jami’an hukumar NIWA na daga cikin bakin da suka halarci daurin auren Fatiha ta Babban Manajan Kamfanin NIWA, Dan Alhaji JIbril Darda’u, Barr. Darda’u JIbril da Hajara Mu’azu wanda ya gudana a Lokoja ranar Asabar.

Daurin auren wanda ya gudana a gidan marigayi Alhaji Mu’azu Sarkin Fawa Yaro, Lakwaja, babban limamin Lakwaja , Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban ne ya jagoranci bikin.

See also  Dan Malikin Lakwaja Ya Yabawa Maigarin Lakwaja Kabir Maikarfi 1V

Sha’aban, wanda ya daura auren bayan an cika dukkan sharuddan auren Musulunci da kuma biyan Sadaki da wakilin angon, ya yi Kira gaiyaye da su koya wa ‘ya’yansu ka’idojin addinin Musulunci.

DCP Ahmed a wata hira da manema labarai, ya taya ma’auratan murnar auren fatiha da kuma mai cike da tarihi.

Ya Kuma umarce su da su ci gaba da addu’a, su ji tsoron Allah, su mutunta alkawuran aurensu don tabbatar da dawwamammen zaman lafiya da jin dadi a cikin dangantakarsu.

Uban angon, Alhaji Darda’u wanda ya cika da dimbin farin Ciki,ya nuna jin dadinsa ga dukkan wadanda suka halarci taron.

Hotuna daga bikin

See also  Speech presented by His majesty,King Saidu Akawu Salihu,The Ohimegye Igu of Igu Kingdom,on the occasion presentation of staff of office by the Kogi state Governor, Alhaji Yahaya Adoza Bello, Wednesday 24th of January 2024.
Visited 16 times, 1 visit(s) today
Share Now