Mu’azam ya Shira Adu’a Fidau don Marigayi Shugaban karamar hukumar Lakwaja Majalisar

Daga Musa Alfaki Muhammad Nasidi

Honorabul Mu’azam Bashir, jigo a jam’iyyar APC na ward D, karamar hukumar Lakwaja, a ranar Litinin ya shirya addu’a ta musamman ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Lokoja, Marigayi Hon. muhammad Danasabe Muhammad wanda ya rasu ranar Juma’ar da ta gabata a asibitin Shifa dake Lakwaja, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Masallacin Dan Kano unguwar Kura, cike yake da jama’a da suka zo addu’ar Muhammad Danasabe Muhammad.

Addu’ar wadda khalifa Yahaya Babadoko Soje ya jagoranta ta samu halartar jiga-jigan jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Hon Maikudi Bature, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lakwaja, Hakimi na ward D, Malam Isah Baba Nasidi, Supervisory Council Of Education, Hon. Hamisu Dan Musa da Protokol na Kakakin majalisar jaha, Hon Salisu Datti da sauran su.

See also  Five killed as soldiers, commercial drivers clash in Kwara

Da yake zantawa da wakilinmu, Mu’azam Bashir ya bayyana marigayi Shugaban a matsayin hazikin shugaba mai kaunar al’ummarsa kuma ya mutu yana yi wa al’umma hidima ba tare da son kai ba.

Ya yi kira ga shugabanni, musamman masu rike da mukaman siyasa da su yi koyi da Marigayi Muhammad Danasabe Muhammad Da yake jaddada cewa marigayin ya taka rawar gani kuma ya bar fagen da karimci.

Ya yabawa shugaban kungiyar SUBEB, comrade Abdullah Suleiman Ndalayi, wanda ya bayyana a matsayin mai taimakon jama’a, shugaban jam’iyyar APC kuma mai wayar da kan jama’a.

Shugaban jam’iyyar APC Bature a nasa jawabin, ya ce tabbas al’umma za su yi kewar marigayi Ciyaman din, Muhammed Danasabe Muhammed, wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban karamar hukumar Lakwaja.

See also  Kogi Flood: NGO Assists 800 Flood Victims In Ibaji

Ya ce “Shugaba babban aboki ne kuma mai ba da shawara mai kishin bil’adama sannan kuma ya taka rawar da ya taka wajen ci gaban al’umma”.

Tun da farko, Khalifa Soje a cikin hudubarsa ya hori shugabanni da su yi wa bil’adama hidima da tsoron Allah.
“Dole ne mu yi hidima da tsoron Allah, mu himmantu wajen samar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban al’ummarmu kafin ranar kiyama.” Inji shi.

Ya roki Allah ya gafarta wa muhammad Danasabe Muhammad dukkan kurakuran sa, ya ba shi janatul-firdaus.

Ga iyalai da abokan arziki da daukacin karamar hukumar Lakwaja, Soje ya yi addu’ar Allah ya ba su ikon jure wa wadanda ba za su iya maye gurbinsu ba.

Visited 7 times, 1 visit(s) today
Share Now