Daga Wakilin Mu By News Desk
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu yace shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar gudanar da sahihin zabe, yana mai tabbatarwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) cewa ba za ta yi katsalandan a zaben gwamnonin Bayelsa, Kogi da Imo ba.
Ribadu ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Juma’a a lokacin da ya gana da shugaban INEC Mahmood Yakubu tare da kwamishinonin hukumar na kasa da sauran mambobin kwamitin tuntubar hukumomin tsaro kan harkokin zabe.
“Wannan zaben zai fi na baya. Za a yi ba tare da tashin hankali ba, za a yi adalci kuma ba za a yi tsangwama ba,” Ribadu ya shaida wa taron.
Ya kara da cewa Tinubu a shirye yake ya marawa Hukumar baya domin samun nasarar yin hakan.
Taron wanda aka gudanar a ofishin NSA da ke Abuja, wani bangare ne na tarukan tuntubar da hukumar ta yi gabanin atisayen da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.
A baya dai INEC ta tabo batun tsaro gabanin zaben a wani taron da ta yi da jam’iyyun siyasa.
Tsaron masu kada kuri’a, muhimman kayan zabe, da kuma kare wuraren tattara kuri’u na daga cikin abubuwan da shugaban INEC ya gabatar yayin taron na ranar Juma’a.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su yi taka-tsan-tsan da masu haddasa rikici a ranar zabe.