Daga Aliyu Abdulwahid
A daren Lahadin da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawa da gwamnonin wasu gwamnonin Arewa biyar da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali a makwabciyar kasar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi na hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin kwanaki 7 da shugabannin kungiyar ECOWAS suka bayar ga gwamnatin mulkin soja ta fice daga ofis ko kuma su fuskanci sojoji da sauran su.
Gwamnonin Arewa a wajen taron da Shugaba Tinubu ya yi a gidan gwamnati sun hada da Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato, Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Gwamna Idris Nasir na Jihar Kebbi da Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina.
Ana ci gaba da fuskantar rashin tabbas kan mataki na gaba da shugabannin kungiyar ECOWAS za su dauka kan barazanar daukar matakin soji a jamhuriyar Nijar, baya ga wasu takunkumi.
Wasu kasashen yammacin Afirka sun bayyana goyon bayansu ga Nijar dangane da harin soji da dakarun ECOWAS ke kaiwa.
A wani rahoto da jaridar THEANALYSTNG ta fitar a baya, an gano wasu jihohi bakwai na arewacin kasar da ke da iyaka da jamhuriyar Nijar na cikin hatsarin barkewar yaki a makwabciyar kasar. Watakila dai shugaba Tinubu ya kira taron ne da gwamnonin jihohin kasar biyar da ke kan iyaka domin la’akari da hadarin da ke faruwa a yankin arewacin Najeriya.