SDP Kogi Ta Rabe Kansa Daga Gamayyar ‘Yan Adawa,Injin Ajaka

Daga THEANALYSTMEDIA

A ranar Asabar din na ne jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi ta balle daga jam’iyyar adawa ta ADC.

Dan takarar Gwamna na Jam’iyyar a 2023, Alhaji Muritala Ajaka ne ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki, wanda aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Lakwaja, Jihar Kogi.

Ya kira dan yayan jam’iyyar da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa jam’iyyar ta ruguza tsarinta.

A cewar sa “SDP ita ce jam’iyyar da za ta doke sauran Jami’u a Kogi” yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta mayar da hankali ne wajen samar da dabarun wargaza jam’iyyar All Progressives Congress a dukkan matakan shugabanci a babban zabe na 2027.

See also  Substitution Primary: Kogi SDP Submits Nominees for Governor, Deputy to INEC

Ya kuma jaddada hadin kan shugabanni da masu ruwa da tsaki a jihar inda ya kara da cewa “babu wani bangare a kogi SDP, Ahmed Attah shine shugaba tare da Idris Sofada a matsayin sakataren jiha.”

Ajaka ya tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyyar SDP kudirin ceto Nijeriya daga hannun gwamnati mai ci da kuma samar da gwamnati mai kishin kasa a kowane mataki.

Taron wanda ya samu halartar mambobin kwamitin ayyuka na jiha, ya samu halartar Alhaji Muritala Ajaka, mataimakinsa dan takarar gwamna, Cif Ranti Abenemi, shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Ahmed Attah, Sakatare, Hon. Idris Sofada da Hon. Ali Ajuh.

Visited 18 times, 1 visit(s) today
Share Now