Sarkin Fawan Lakwaja Idi, Yayi jimamin Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo

Daga Wakilin Mu.

ALHAJI IDI IBRAHIM, SARKIN FAWAN LAKWAJA.

Sarkin Fawan Lakwaja, Alhaji Idi Ibrahim ya yi jimamin rasuwar mahaifin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Momoh Sani Ododo wanda ya rasu a jiya Litinin a Abuja.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu tare da mika wa THEANALYSTMEDIA a Lokoja a ranar Talata, Idi ya bayyana rasuwar Momoh Sani a matsayin babban rashi kuma ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.

Sarkin fawa, wanda ke Ta’aziyyar Gwamnan kogi ya ci gaba da cewa, “Rasuwar Alhaji Ahmed Momoh Sani Ododo ba rashi ce ga iyalansa musamman ba, har ma ga daukacin al’ummar Musulmi da Jihar Kogi baki daya.

Ya roki Allah da ya baiwa gwamna hakurin jure rashin maye gurbinsa ya kuma baiwa Alhaji Ahmed janadul-firdaus.

Visited 3 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  MNJTF Ta Daku she Harin A' Garin Magunu, Ta Kashe Yawan 'Yan Ta'addar ISWAP