Daga Musa Tanimu Nasidi
Allah ya yi wa Alhaji Isma’il Abdukareem Dan Buran na Lakwaja rasuwa.
Abdukareem ya rasu yana da shekaru 75 a duniya a asibitin kasa Abuja a ranar Laraba 6 ga watan Agusta, 2025 bayan ya sha fama da jinya.
Tsohon kwamishinan INEC kuma wani lokaci mai kula da ayyuka a rusasshiyar karamar Hukuman Kogi, ya bar mata biyu da ‘ya’ya da jikoki.
Za a tuna da marigayi Dan Buram bisa sadaukar da kai ga al’ummar Lakwaja.
Allah ya gafarta masa dukkan kurakuran sa, ya saka masa da janadul-firdaus, ya baiwa iyalai da al’ummar Lokoja da daukacin al’ummar musulmi kwarin gwuiwar jure rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba. Ameen.
Visited 13 times, 1 visit(s) today