Injiniya Gegu Ya Gabatar Da Sabuwar Mota Ga Maigarin Lakwaja, Maikarfi 1V

Daga Musa Tanimu Nasidi

A ranar Litinin da ta gabata ne kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa na jihar, Injiniya Abubakar Bashir Gegu ya mika motar kirar Toyota Land Cruiser ga Maigarin Lakwaja, Mai Martaba,Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V.

Da yake mika mukullin motar ga sarkin a fadarsa, Gegu ya bayyana cewa manufarsu ita ce a amince da gwamnatin Maigari a matsayin masu taimakawa da zaman lafiya da tsaro da ci gaba a masarautar da ma jihar baki daya.

“Mai martaba sarki, gwamnatin Gwamna Usman Ododo ta fahimci mahimmancin cibiyoyi na gargajiya.

Da wannan ƙaramar kyauta, za mu ba da gudummawa don magance matsalar sufuri ta Mai Martaba Sarki.

See also  Cigarin Lakwaja,Sunusi Ya daukaka Zuwa "SARKIN SUDAN" Lakwaja

“A magana ta gaskiya, gwamnatin Gwamna Ododo ta san irin abubuwan da sarakunan gargajiya suke yi domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’ummarsu, “Ina girmama cibiyar gargajiya ta Lakwaja a matsayin tushen hadin kan al’umma, zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummarmu,” in ji Gegu.

Sarkin ya gode wa Injiniya Gegu da wannan kyautar, inda ya bayyana shi a matsayin “mai kishin kasa kuma mai taimakon jama’a.”

Visited 4 times, 1 visit(s) today
Share Now