Dan Malikin Lakwaja Ya Yabawa Maigarin Lakwaja Kabir Maikarfi 1V

Daga Musa Tanimu Nasidi

Mai martaba Sarkin Lakwaja.

Sabon Dan Malikin Lakwaja, Mai Ritaya CIF Sufirtendant Hukumar Kwastam ta Najeriya, Alhaji Muhammad Danladi Abdulsalam, ya yabawa mai martaba Maigarin Lakwaja, Shugaban Masarautar Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, bisa karramawar da aka yi masa da iyalansa.

Dan Maliki, ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis a Lakwaja.

Abdulsalam bayyana Maigari a matsayin uba wanda tsarin shugabancinsa ba ya misaltuwa.

Ya kuma tabbatar wa Sarkin da ‘yan Majalisar Masarautar kan kudirinsa da kuma shirye-shiryen tabbatar da amincewar da aka yi masa na Dan Malikin Lakwaja.

” A madadina da daukacin iyalaina, wadanda aka karrama, ina mika godiyata ga Mai Martaba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, da ya same ni na cancanci wannan karramawa, kuma ina kara tabbatar wa mai martaba Sarkin cewa hakan zai kara zaburar da ni wajen gudanar da ayyukana ga jama’a.

See also  Eid-el-Kabir: Shehu Fikara felicitates with Muslim faithfuls

“Ina so in nuna matukar godiyata ga abokai, ‘yan majalisar gargajiya na Lakwaja bisa ga irin goyon baya da karfafa gwiwa da suka bayar a tsawon wannan lokaci,” in ji shi.

Visited 20 times, 1 visit(s) today
Share Now