

Daga Musa Tanimu

Malikin Lakwaja, Alhaji Danladi Abdulsalam ya taya Sakataren Majalisar Malamai na Jihar Kogi kuma tsohon Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kogi, Alhaji Baba’ango Idris murnar nadin da Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya yi masa a matsayin Amirul Hajj.2025.
Sakon na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dan Maliki a ranar Talata kuma ya mikawa jaridar TheEANLYSTNG dake Lakwaja cewa nadin tsohon sakataren zartarwa ya samo asali ne daga irin kwazonsa, jajircewa da rikon amana.
“Ina da kwarin gwiwa da kuma fatan Alhaji Baba’ango Idris zai kawo arziƙin iliminsa da gogewarsa wajen gudanar da wannan gagarumin aiki”. Yace.
Abdulsalam ya kuma yi kira ga Amirul Hajj 2025 da ya ba da hujjar amincewar da gwamnatin jihar Kogi ta yi masa na ganin ya yi aikin hajjin 2025 zuwa Saudiyya cikin nasara ba tare da cikas ba.
Ya yi masa addu’ar samun nasara da kuma shiriyar Allah wajen gudanar da aikin da aka dora masa.