Jigon PDP a Kogi Abdullahi Yusuf Abdullahi ya koma APC

Daga Musa Tanimu Nasidi

Wani fitaccen jigon jam’iyyar PDP a karamar hukumar Lakwaja, Malam Abdullahi Yusuf Abdullah, wanda aka fi sani da Malam BAMA, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Da yake sanar da sauya shekarsa a Lakwaja ta wata wasika da da kansa ya sanya wa hannu, wanda ya aike wa shugaban jam’iyyar a ranar Juma’a, Abdullah ya gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ya samu na yin aiki.

Ya ci gaba da bayyana cewa: “Bayan na yi nazari sosai, na yanke shawarar cewa ya fi dacewa da burin kaina da na sana’a na ficewa daga jam’iyyar.” Yace.

See also  Barr. Ahmed Ya Taya Ganduje Murnar Nadashi A Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa

Wasikar da THEANALYSTNG ta samu, ta aikewa shugaban jam’iyyar kamar haka: WASIKAR FICEWA DAGA PDP

“Don Allah ku karbi wannan wasika a matsayin sanarwar ficewa daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) jihar Kogi daga yau Juma’a 14/2/2025.

Na yaba da damar da na samu a lokacin da nake zama dan PDP

Duk da haka bayan na yi la’akari da kyau, na yanke shawarar cewa ya fi dacewa da burin kaina da na sana’a don sauka daga jam’iyyar.

Na gode da fahimtar ku, ina yi wa jam’iyyar fatan ci gaba da samun nasara a ayyukanta na gaba”.

Naku gaskia har abada

Mallam Abdullahi Yusuf Abdullahi.

Visited 12 times, 1 visit(s) today
Share Now