Daga Musa Tanimu Nasidi.
Mai martaba Maigari Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, ya yi kira ga ‘yan jihar da su marawa gwaunatin mai girma, Gwauna Ahmed Usman Ododo baya, inda ya bukaci ‘yan kasar da su kara zage dantse Zaman lafiya da hadin kai da fatan alheri.
A wata sanarwa da mai martaba sarkin ya sanyawa hannu a ranar Lahadi a Lakwaja, Kuma ya rabawa manema labarai Maigarin ya taya Gwamna Ododo da gwamnatinsa murnar cika shekara daya a kan karagar mulki tare da yin kira ga ‘yan jahar kogi da su baiwa gwamnati albarka da goyon baya.
Ya bayyana fatansa na samun nasarar gudanar da mulki a gwamnatin Ododo.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mai martaba Maigari na Lakwaja kuma shugaban majalisar sarakunan karamar hukumar Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, yana mika sakon fatan alheri ga gwamna Ahmed Usman Ododo kan cikar shekara ta farko a kan karagar mulki.
“Mai martaba Sarkin ya yi kira ga daukacin al’amuransa da ’yan majalisarsa gaba daya da su ci gaba da karfafa aikin zaman lafiya da hadin kai da kuma fatan alheri.
“Ya kuma yi kira gare su da su baiwa gwamnatin Ododo albarka da goyon baya domin ta samu nasara a kokarinta na gina jihar Kogi a cikin burinmu.
“Maigarin ya bayyana fatansa na samun nasarar gudanar da mulki daga gwamnatin Alhaji Ahmed Usman Ododo.”