Maigari Lakwaja ya ba da gudummawar magunguna, da ake amfani da su ga PHC guda uku a Lakwaja

Daga Musa Tanimu Nasidi

Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi IV, a ranar Litinin ya ba da gudummawar magunguna da sauran kayan masarufi na miliyoyin naira ga asibitocin kiwon lafiya na matakin farko guda Uku da ke Anguwar Yashi, Anguwan Kura da Kabawa a Lakwaja babban birnin jihar.

Wannan karimcin na daga cikin ayyukan da aka shirya na bikin cika shekara guda na basaraken gargajiya mai daraja ta daya a kan karagar mulkin kakanninsa .

Da yake jawabi a asibitocin guda uku, Maigari, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da cewa asibitocin sun samar da ingantaccen kiwon lafiya ga mazauna yankunan.

See also  Labaran Hotuna:

Ya kuma bukaci ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko da su yi iya kokarinsu wajen samar da kiwon lafiya ga al’umma, inda ya ba da tabbacin cewa cibiyar gargajiya ta Lokoja za ta ci gaba da tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na Lokoja.

A jawabinsa na godiya shugaban karamar hukumar Lakwaja ,Hon. Abdullahi Adamu ya godewa Maigarin Lakwaja bisa wannan tallafin, yana mai cewa kokarin zai karawa kokarin gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar.

Ya kuma gargadi ma’aikatan lafiya da ke asibitocin da kada su sayar da kayayyakin saboda kowane dalili, yana mai jaddada cewa ya kamata a rika ba marasa lafiya magungunan kyauta.

See also  Shugaban Sabuwar kasuwar Lakwaja ya yabawa Maigari

Hon. Adamu ya yi addu’ar Allah ya kare shi ya kuma yi masa jagora ya ba shi damar wanzar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaban da aka samu a gidansa a lokacin mulkinsa.

Maigarin Lakwaja,Tare Da Daman Lakwaja, Baba Sule
Visited 9 times, 1 visit(s) today
Share Now