Daga Musa Tanimu Nasidi
Shugaban kungiyar sufurin babura ta Najeriya reshen karamar hukumar Lakwaja, Comrade Abdulrahman Abubakar, a.k. a Baba sauti, ya yabawa Gwamna Ahmed Usman Ododo .
Shugaban ya yi wannan yabon ne a ranar Litinin din da ta gabata, a ofishin sa yayin da ake ci gaba da yin rijistar tantance mahaya Okada, mai taken “Kogi state compulsory gane management” wanda ma’aikatar sufuri ta jihar ta shirya.
Kwamared Sauti ya ce kungiyar ta bibiyi ayyukan ci gaba a jihar tun bayan hawan Gwamna Ahmed Usman Ododo, ta aiwatar da manufar bunkasa harkar sufuri ta hanyar ma’aikatar sufuri don amfanin kowa.
Ya kuma yi nuni da cewa Ododo ya yi kyau tun daga farkonsa, don ci gaban jihar, kuma “sun jajirce wajen goyon bayan manufofi da tsare-tsare na Gwamna.
Dangane da rajistar masu tuka Okada a Lakwaja babban birnin jaha, Sauti ta yi kira ga mambobin kungiyar da su fito su yi rajista.
“Dole ne dukkan mambobi su yi rajista da kungiyar ta ofishina, mun samu kungiya daya da ma’aikatar sufuri ta bayar da fom ga ofishina a matsayina na shugaban kungiyar sufurin babur ta Najeriya reshen karamar hukumar Lakwaja,” inji shi.
Ya kuma yi gargadin cewa duk dan kungiya da ya gaza yin rajista da ofishinsa, ba za a bar shi ya yi aiki a babban birnin jihar ba.
Baba Sauti ya yabawa shugaban karamar hukumar Lakwaja, comrade Abdullahi Adamu bisa yadda yake nuna salon shugabanci nagari.