Shatiman Lakwaja Kasim, Dama Sulaiman,Sadaukin Lakwaja sun halarci daurin auren Dan Marigayi Abubakar Ola

Daga Wakilinmu

Hon. Ibuku Muhammad Ola addressing Journalists

Manyan masu rike da sarautar gargajiya na Lakwaja, da sauran manyan baki a ranar Juma’a sun mamaye Lakwaja, domin halartar daurin auren dan marigayi Abubakar Ola, MALLAM ABUBAKAR OLA YUSUF da kuma masoyin matarsa, MALLAMA ABDULAZEEZ ONIZE ZAINAB.

An gudanar da daurin auren ne a masallacin Alhaji Ismail Otaru, fentolu a Lakwaja.

Malam Abdulsalam Salaudeen ya baiwa ‘yarsa, Oniza Zainab ga wakilin angon, Muhammed ya-mala bayan an biya sadaki N100,000.

Manyan Malaman Addinin Musulunci da dama ne suka halirci bikin, Wanda babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwan Kura, Sheikh Abubakar Adamu ya jagoranta

Daga cikin malamai akwai Imam Ibrahim Nyass Yusuf Abdullah, Khalifa Ibrahim Etsu Shuiabu Kenchi,Malam Abdulrahman Danladi Kabawa da limamin masallacin Alhaji Ismail Otaru da dai sauransu.

See also  Maigarin Lakwaja yana taya al'ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekara ta 1446

Manyan baki a bikin auren sun hada da: Daman Lakwaja, Alhaji Sulaiman Baba, Rafin Lakwaja,Alhaji Inuwa Shugaba, Shatiman Lakwa, Alhaji Muhammad mabo Kasim da Sadaukin Lakwaja, Alhaji Bama Mudi

Malaman addinin Musulunci da suka gudanar da taron sun yi addu’ar zaman lafiya da hadin kan ma’auratan, kamar yadda suka nemi tsarin Allah ga shugabannin kasa.

Visited 29 times, 1 visit(s) today
Share Now