Bikin sabuwar shekara: Shugaban karamar hukumar Lakwaja ya hana kona tayoyi, tare da toshe hanyoyin shiga

Musa Tanimu Nasidi

Shugaban karamar hukumar Lakwaja, Comrade Abdullahi Adamu, ya gargadi jama’a da su daina kona tayoyi da toshe hanyoyin shiga da jefa bama-bamai da sunan maraba da 2025.

Adamu, ya yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Comrade Iliyasu Zakari, kuma ya rabawa manema labarai ranar Talata, a lakwyaja.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“A yayin da ake tunkarar bukukuwan sabuwar shekara, ofishin shugaban karamar hukumar Lokoja, ya bukaci mazauna yankin da su guji kona tayoyi da sauran abubuwa masu cutarwa da ka iya kawo barazana ga muhalli da kare lafiyar jama’a.
Shugaban, Comrade Abdullahi Adamu, ya nuna damuwa game da hadarin da ke tattare da irin wadannan ayyuka, kuma yana kira ga kowa da kowa da ya hada hannu wajen kare ababen more rayuwa na jama’a, da inganta muhalli mai aminci da lafiya.

See also  Shatiman Lakwaja Kasim, Dama Sulaiman,Sadaukin Lakwaja sun halarci daurin auren Dan Marigayi Abubakar Ola

Ofishin shugaban ya himmatu wajen ganin an gudanar da bukukuwan sabuwar shekara cikin jin dadi da walwala kuma ba tare da wata matsala ba, kuma tana hada gwiwa da hukumomi da masu ruwa da tsaki domin cimma wannan buri.

An shawarci mazauna yankin da su nemo hanyoyin da za su bi don murnar sabuwar shekara ta hanyar samar da yanayi mai kyau da ban sha’awa wanda ke da daɗi ga kowa da kowa, tare da kare muhallinmu da amincin jama’a.”

Visited 5 times, 1 visit(s) today
Share Now