Magajin Garin Lakwaja Kenchi,Yabawa Senator Karimi

Daga Aliyu Musa Nasidi.

Magajin Garin Lakwaja, Khalifa Ibrahim Etsu Shuiabu Kenchi, ya yabawa sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma, Sanata Sunday Karimi, bisa jagorancin sa musamman wajen samar da zaman lafiya.

Khalifa Kenchi ya yi wannan yabon ne a zawiyya Sheikh Shuiabu Kenchi a lokacin da dan majalisar ya kai masa ziyarar ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyasa , Sayyida Aminah a Lakwaja. Kafanchan, Jema’a local

Ya bayyana cewa tun da Sanata Karimi ya hau kujera sanato ya tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar mazabar Kogi ta yamma ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Ya bayyana ziyarar ta’aziyyar a matsayin mafi kyawu da aka taba yi masa da iyalansa.

See also  Comrade Adamu Ya Bukaci Hadin Kai, Zaman Lafiya A Yayin Da Kungiyar Matan Lakwaja Ta Yi Maulidi

Yayin da yake godiya ga sanatan, Kenchi ya yi addu’ar Allah ya mayar da Karimi Abuja lafiya.

Visited 12 times, 1 visit(s) today
Share Now