Daga Musa Tanimu Nasidi
A ranar Juma’a 9 ga watan Nuwamba 2024 ne aka shirya yin Fida’u ta kwanaki bakwai ga Sayyida Aminah Sheikh Shuiabu Kenchi kuma mahaifiyar Khalifa Ibrahim (Etsu) Sheikh Shuiabu Kenchi Magajin Garin Lakwaja.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Magajin Garin Lakwaja, Khalifa Ibrahim (Etsu)Sheikh Shuiabu Kenchi ya ce za a yi addu’ar ne a zawiyya Marigayi Sheikh Shuiabu dake cantonment da karfe tara na safe.
Sanarwar ta ce babban limamin Lakwaja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban ne zai jagoranci addu’ar, kuma malaman addinin musulunci na ciki da wajen jihar za su taimaka musu.
Hajiya sayyida Amina Shuiabu Kenchi, ta rasu a ranar Juma’ar da ta gabata bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya, ta rasu ta bar ‘Ya’ya da dama da suka hada da, khalifa Etsu Ibrahim sheikh Shuiabu Kenchi, jikoki da Jikoki da dama.
Tuni dai aka binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar Musulmi ta Unguwan Kura, Lakwaja, Jihar Kogi.
Allah ya gafarta mata dukkan kurakuranta, ya sanya ta Cikin janatul-firdaus, ya baiwa iyalai karfin gwiwa da juriyar da batattu, ameen.
Sa hannu; Magajin Garin Lakwaja, Khalifa Ibrahim (Etsu) sheikh Shuiabu Kenchi.