Daga Musa Tanimu Nasidi
Mambobin kungiyar ‘yan banga na Upper-Garage, sun kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin awaki ne, Nda Joseph mai shekaru 23 da Ahmed Yunusa dan shekara 33 da ake zargin sun saci akuya a Unguwan.
Shugaban ’yan banga a yankin, Danjuma Ibrahim ya ce an kama Joseph ne bayan da ya yi yunkurin kai wa Ahmad Yunusa bunsuran da ya sace a gidansa da ke Unguwan Kura da karfe 11:30 na daren ranar Talata.
Ya ce ‘yan banga al’umma ne suka sauke su sannan suka nufi hanyar da za a dauka nan take suka kama mutanen biyu.
Ya zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto, mutanen biyu suna hannun ‘yan banga, inda suka yi alkawarin mika su ga ‘yan sanda domin ci gaba da yi musu tambayoyi.
Visited 13 times, 1 visit(s) today