Gwauna Ododo ya nada Babadoko da sauran su a matsayin kwamishinonin hukumar kananan hukumomin jaha

Daga Musa Tanimu Nasidi

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya zabi tsohon dan majalisar dokokin jihar Kogi mai wakiltar mazabar Lakwaja I, Honarabul Suleiman Babadoko a matsayin kwamishina a hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi ta jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon. Aliyu Umar Yusuf mai dauke da sa hannun gwamna Ahmed Usman Ododo a ranar Talata a lokoj.

Shawarar, a cewar wasikar ta zo daidai da tanade-tanaden sashe na 4 (2) na hukumar ma’aikatan kananan hukumomin jihar Kogi.

Haka kuma an zabi Adabenege Adams a matsayin shugaba, Elisha Folorunsho (Kwamishinan Yamma), Amodu Yakubu da Attai Okolo Musa (Kwamishinonin Kogi ta Gabas), da Salami Abdulraheem (Kwamishina, ta Tsakiya).

See also  Kwamishinan Albarkatun Ruwa Injiniya Farouk Ya Gudanar Da Tattaunawa Akan Shirye-shiryen Gwamna Ododo Akan Samar Da Ruwan Sha

Sa hannu:
Yabagi Mohammed,
Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaban Majalisar,
Majalisar dokokin jihar Kogi.

Visited 16 times, 1 visit(s) today
Share Now