Alhaji Muhammad Mabo Kasim ( Shatiman Lakwaja) Da Marigayi Dr. Umar Farouk Abdulazeez ( Tafida na Ebira)

Shatiman Lakwaja, Alhaji Muhammad Mabo Kasim, yana mika gayyata ga jama’a zuwa wajen daurin auren ‘yarsa, Rahman Muhammad Kasim.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a Lakwaja da kansa kuma ya mika wa manema labarai a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce; “Muna farin ciki da gayyatar ku da abokan arziki da sauran jama’a zuwa wajen daurin auren ‘yarmu, Rahma Muhammad Kasim da Abduljabbar Abdulazeez Adeiza wadanda ke shirin fara sabuwar gogewa a rayuwa tare da daura aure a matsayin mata da miji.

An shirya daurin auren a ranar Asabar 26 ga Oktoba, 2024 da karfe 10 na safe.

Wuri: No 9 Walter Bakie Street ( Shabayagi Quater’s) Lakwaja, Kogi state.Za a yi liyafar a Kay – Galaxy Event centre, no 50 old Okene – Lokoja Road, Lakwaja,jahar Kogi, nan da nan bayan auren .

See also  Farouk, yayi alkawarin aiwatar da manufar Gwamna Ododo akan jihar Kogi

Allah Ya albarkace ku baki daya kamar yadda kuka girmama gayyatarmu. JazakaAllahu Khairan ka kasance mai albarka da rahma zuwa inda kake.

Sa hannu; Muhammad Mabo Kasim, Shatiman Lakwaja.

Visited 27 times, 1 visit(s) today
Share Now