Rashin Tsaro: Gwamna Ododo Ya Karfafa Mafarauta Da Kayan Aiki

Daga Musa Tanimu Nasidi

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo a ranar Alhamis ya baiwa mafarauta a jihar kayan aikin tsaro a wani bangare na kokarin gwamnati na inganta tsaro a jihar kogi.

A wajen bikin mika kayan a gidan gwamnati a Lakwaja, gwamna Ododo, ya ce kayan aikin za su taimaka wa jami’an tsaro da mafarautan wajen gudanar da sa ido da tattara bayanan sirri da za su saukaka ayyukan hukumomin tsaro a jihar.

Ya kuma yi bayanin cewa kayan aikin za su taimaka wa mambobin kungiyar mafarauta don isa ga wurare masu wahala.

Ya yabawa shugabannin kungiyoyin bisa sadaukarwa, jajircewa da goyon bayan da suke baiwa hukumomin tsaro a jihar.

See also  Covid-19 Second Wave: Nigerian govt blames churches, schools for COVID-19 second wave

Visited 20 times, 1 visit(s) today
Share Now