Maigari Ya Bawa Ali sarautan Gargajiya GALADIMA FAWA

Daga Aliyu Abdulwahid

Mai martaba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, ya baiwa Alhaji Ali Muazu, aka Ali Zaki sarautar Galadiman Fawa Lakwaja.

An sanar da hakan ne a cikin wata takardar nadi mai dauke da sa hannun Alhaji Muhammad Usman Nalado, sakataren karamar masarautar Karamar Hukumar Lakwaja, mai kwanan wata 15 ga Yuli, 2024.

Sanarwar ta kara da cewa, ”Muna godiya da irin ayyukan da ka yi na sadaukar da kai wajen bunkasa sana’ar ku mai daraja, masarautar Lakwaja , majalisar masu rike da sarautar gargajiya da kuma kaunar ka ga al’ummar yankinmu”.

“Da wadannan da ma wasu da dama, muna farin cikin karrama ka da sarautar gargajiya ta Galadiman Fawan Lakwaja a matsayin wata alama ta musamman na yabawa da karfafa gwiwa domin samun ci gaba ga bil’adama baki daya da ma masarautar Lakwaja musamman masarautar Lakwaja ‘ sanarwa ta ƙare.

See also  Labaran Hotuna:
Visited 16 times, 1 visit(s) today
Share Now