Barrister Inuwa Taya Sarkin Fawan Lakwaja Idi, Galadima Fawan Ali murna

Daga Alfaki Muhammad Nasidi

Sakataren hukumar kula da otal-otal da yawon bude ido na jihar Kogi, Barista Muhammad Sani Inuwa a ranar Lahadi, ya taya Idi Ibrahim, sabon Sarkin Fawan Lakwaja da takwaransa, Alhaji Ali Muazu bisa nadinsa Galadima Fawan da Mai Martaba Sarkin Lakwaja, Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi Na hudu.

A cikin sakon taya murna da ya sanya wa hannu kuma ya mika wa ‘yan jarida a Lakwaja, Barista Inuwa ya yi musu fatan alheri da zaman lafiya a cikin ayyukansu daban-daban.

Ya kuma yi kira ga duk wadanda suka yi takara da su yi aiki tare da sabon Sarkin Fawan Lakwaja domin samun zaman lafiya, da kuma ba shi damar ciyar da sana’arsu zuwa ga kololuwar ci gaba.

See also  PROFILE OF SHANTALIN LAKWAJA, ALHAJI BALA MUHAMMAD HARUNA

“Allah ya sa mulkin ku ya ci gaba da kawo ci gaba, da wadata, da zaman lafiya a masarautar Lokoja da ma jihar baki daya” Inuwa.

Visited 34 times, 1 visit(s) today
Share Now