Daga Musa Tanimu Nasidi
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar sabuwar kasuwar Lakowaja, Alhaji Sani Inusa ya yabawa Mai Martaba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, bisa kaddamar da kwamitin tantance SARKIN KASUWA.
Inusa ya yi wannan yabon ne a ranar Litinin a wajen taron kaddamar da kwamitin da Maigarin Lakwaja, ya yi na tantance shugaban ‘yan kasuwa ko Sarkin kasuwa, wanda zai wakilci ‘yan kasuwar Lakwaja masarautar Lakwaja.
Inusa, wanda ya jagoranci tawagar zartaswar kungiyar yan kasuwar Lakwaja, ya ce matakin nada Sarkin kasuwa da Mai Martaba ya yi abin farin ciki ne.
Ya ce a matsayinsa na shugaban kungiyar ‘yan kasuwa; “Mu namu ne mu ba wa kwamitin zaɓen Sarkin kasuwa shawara, cewa dole ne sabon Sarkin ya kasance mutum wanda ya kware, sanin kasuwa, da shugabanni waɗanda za su kiyaye mutuncin majalisar gargajiya” Inji Shi.
Tun da farko a jawabinsa na bude taron, shugaban kwamatin kuma Hakimi na ward B, Alhaji Ahmed Bala Sarkin zango ya ce ,Maigarin Lakwaja,mai Martaba Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, a kwanan baya ya kaddamar da kwamitin da Zai zabo Sarkin Kasuwa wanda Zai wakilce Yan Kasuwa a majalisar masarautar Lakwaja.
Ya bayyana cewa kamar sauran garuruwan arewacin kasar nan, duk kasuwanni suna da Sarkin kasuwa wanda a cewar Sa, “sarakuna ke nada Su da kuma Sanya su wakilcin majalisar masarautu ,yana mai jaddada cewa Lakwaja ba za ta bambanta ba da takwaruren ta ba wajen nada sarkin Kasuwa a kasuwanin mu” Sarkin zango ya ce.
“A halin yanzu wadanda ke rike da madafun iko a kasuwanninmu ma’aikatan kananan hukumomi ne, ba ‘yan kasuwa ba ne suka nada su ko suka zabe su, haka kuma ba saikin Lakwaja ba ne ya nada su”
Ya ci gaba da cewa majalisar Masarautar tana sane da kungiyar Yan Kasuwa da wakilan shugabanninsu
‘Muna son ku gabatar da dan takara mai karbuwa a tsakaninku domin tabbatar da shi a matsayin sabon Sarkin kasuwa”
Sai dai ya yi gargadin cewa, duk wanda za su gabatar, Sai mai Martaba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, ya amince da shi.
Shugaban kwamitin ya baiwa ‘yan kasuwar zuwa Ranar Alhamis su gabatar da dan takara mai karbuwa.
Zaman Komitin ya Samu Halarta Hakimai da kuma Wakilin Gabas .