Maigarin Lakwaja Ya yabawa Gwamna Ododo bisa gaggauta biyan albashin ma’aikata Da Yan Fansho

Daga Aliyu Abdulwahid

Maigarin Lakwajal kuma shugaban majalisar gargajiya na karamar hukumar Lakwaja, mai Martaba, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, ya yabawa gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi bisa wannan gagarumin shiri da yayi na bunkasa ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a jihar.

Sarkin ya yi wannan yabon ne a wajen bikin Hawan Bariki na bana a bikin Edil-Adha da aka yi ranar Litinin a Lakwaja.

Kabir, wanda ya bayyana irin gagarumin ci gaban da Gwamna Ododo ya samu kan harkokin tsaro ta hanyar sabbin tsare-tsare, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba gwamnan nasara wajen bunkasa jihar.

Maigarin ya yaba da kuma yabawa Gwamnan bisa samar da motocin tsaro a fadin jihar da nufin duba matsalar masu garkuwa da mutane a jihar.

See also  For His Sterling Contributions To National Development, American- European University Honours Aliyu With Doctorate Degree

Ya kuma yi kira ga al’ummomin jihar da su hada hannu da hukumomin da aka kafa, yana mai jaddada cewa “yayin da muke bikin Edi-Kabir, dole ne mu rungumi zaman lafiya, hadin kai da mutunta hukumomin da aka kafa a jihar, kananan hukumomi da kuma kasa baki daya,” inji shi.

Bikin na bana wanda ya gudana a dandalin Muhammadu Buhari dake Lakwaja, ya samu halartar: Babban limamun Lakwaja , sheikh Aminu Sha’aban,Sanata Tunde Ogbeha, shugaban masu rike da sarautar gargajiya na Lakwaja wanda ya samu wakilcin Sodagi na Lakwaja, Hon. Shaba Ibrahim, kwamishinan albarkatun ruwa, Injiniya Muhammad Danladi Yahaya Farouk, shugaban karamar hukumar Lakwaja , Comrade Abdullahi Adamu, Cigarin Lakwaja, DCP Ahmed Muhammad Sanusi da Daman na Lakwaja , Alhaji Baba.Sule.

See also  Wahalhalun Tattalin Arziki: Kog NLC Ta Shiga Tawagarsu A Zanga-zangar

Sauran sun hada da: Maiyakin Lakwaja, Alhaji Ali Lawal Jiya, Shatali na Lakwaja ,Alhaji Bala Haruna da sauran wasu da sauran su.

Visited 29 times, 1 visit(s) today
Share Now