Mawallafin Jaridar THEANALYST na taya Barr. Inuwa a matsayin Sakatare na Kogi Geographic Information Service (KOGIS)

Daga Aminah Shaba

Mawallafin jaridar THEANALYST, Jarida ta yanar gizo, Musa Tanimu Nasidi, ya mika sakon taya murna ga Barista Inuwa Muhammad Inuwa, bisa nadin da Gwamna Ahmed Usman Ododo ya yi ma SA a matsayin Sakataren KOGIS

Ku tuna cewa Gwamna Ododo a ranar Asabar ya nada Barr Inuwa a matsayin sakataren KOGIS.

A cikin wani sakon taya murna da ya sanya wa hannu kuma ya mika wa manema labarai a ranar Lahadi a Lakwaja, ya bayyana nadin Inuwa a matsayin wanda ya cancanta da kuma ban mamaki.

Nasidi ya cigaba da cewa Inuwa Kwarare ne da gogewa a fannin shari’a da al’amuran gudanarwa, jajircewarsa na inganta shugabanci na gari sun sa ya zama cikakke ga wannan nadi na musamman.

See also  Illegal Mining, 2 confirmed dead in Kogi

“Ba ni da tantama, Barr. Inuwa Muhammad Inuwa a matsayin sakataren KOGIS zai kawo sauyi mai kyau kuma zai yi tasiri sosai a gwamnatin Ododo,” in ji Nasidi.

“Har ila yau, ina taya ku murna da wannan nadin da ya cancanta. Ina yi muku fatan alheri a sabon matsayinku.”

Visited 28 times, 1 visit(s) today
Share Now