Za’ayi Addu’ar Fidau Ga Marigayi Jibril Ranar Litinin

Mai Ruhuto: Musa Tanimu Nasidi , Daga Lakwaja

An shirya addu’ar Fidau ta marigayi Alarama JIbril Darda’u, tsohon Janara Manaja yada Labarai na NIWA, a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2024.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Malam Sulaiman Darda’u sarnar asabar a Lakwaja, wanda jaridar THEANALYSTNG ta samu, ta ce za a fara taron addu’ar ne da karfe 8:30 na safe a gidan marigayin na kwakwa.

Ku tuna cewa Alaramma JIbril Darda’u ya rasu ne a safiyar Juma’a bayan gajeriyar jinya. Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Allah ya gafarta masa dukkan kurakuran sa, ya baiwa iyalai da abokan arziki da daukacin al’ummar musulmi kwarin guiwar jure rashin maye gurbinsa..ameen .

Visited 6 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  Edil -fitir : Baba Ali Ya Gargaɗi Musulmi Su Riƙe Ruhi, Asalin Ramadan.