Ohimegye ya jinjinawa Aguye bisa alƙawarin da ya yi na kamalla ayyukan Marigayi Buba JIbril

Daga Musa Aliyu Nasidi

Mai Martaba Sarkin Koton karfe, Dr Sai’du Akawu Salihu, ya yabawa Hon. Suleiman Danladi Aguye, dan majalisar tarayya mai wakiltar Lakwaja da Kogi, ya yi alkawarin kammala ayyukan marigayi Umar Babu Jibril a yankin, wanda kafin rasu SA shekaru shida da suka wuce, ya wakilci mazabar Lakwaja da Kogi a majalisa ta 8.

Sarkin ya yi wannan yabon ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin Aguye da mukarrabansa a fadarsa da ke koton karfe.

Akawu, wanda ya karrama marigayi Jibril, ya ce tsohon dan majalisar ya yi wa al’ummar yankin da yawa aiyoka amma ya koka da yadda wasu da ya bayyana a matsayin “marasa bin doka da oda” suka yi amfani da asibitin miliyoyin Naira da marigayi Rt Hon. Umar Buba JIbril a matsayin aikin mazabar yankin.

See also  Ododo ya kori shugaban Rikon saboda karkatar da abubuwan jin daɗi

“Wannan matakin da ka ɗauka don kammala asibitin da aka yi watsi da shi a cikin yankina abin farin ciki ne, wasu ƴan’uwanmu marasa bin doka suna amfani da kadarorin asibitin da suka haɗa da motar asibiti.

Dauke shi kuma a tabbatar an kammala aikin kuma a yi amfani da shi,” in ji Ohimegye

Tun da farko, Aguye ya sanar da Mai Martaba Ohimege cewa yana cikin fadarsa ne domin bayyana masa aniyarsa na tantance aikin Marigayi Buba JIbril da ke koton karfe da kuma Cigaba daga inda ya tsaya.

Ya tabbatar wa Ohimegye kudirinsa na dorewar daga Inda buba JIbril ya tsaya da kuma kammala wasu ayyuka don jama’arsa.

See also  Alleged Coup Plot :Why SSS invited Fani-Kayode,Says Spokesperson

A cikin tawagar Aguye akwai, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lakwaja, Hon Maikudi Bature, jigo a bangaren kuma shugaban gidan siyasar Buba, Alhaji Muhammad Attati Bozy, tsohon shugaban karamar hukumar Kogi da hadiman majalisa da dai sauransu.

Muhimman abubuwan da ke cikin rangadin tantancewar sun haɗa da, ziyarar da aka yi zuwa asibitin koton karfe da ke kan titin abuja

Visited 24 times, 1 visit(s) today
Share Now