Ohimegye Ya Bada Saratun Gargajiya Wa Tatu, Bako Da Wasu Mutane 23

Daga Musa Tanimu Nasidi

Ohimegye Igu na Masarautar Igu, Dr Saidu Akawu Salihu a ranar Juma’a ya nada manyan mutane 25 masu sarautar gargajiya da suka hada da Ambasada Yahaya Shuiabu Tatu, wanda aka ba shi sarautar OGAZA OGBANI na masarautar Igu, Malam Salihu Bako, Ogazuma OGBANI, Alhaji Shuiabu Musa ,Aronyoga na Masarautar Igu da Alhaji Usman Halilu an ba su sarautar Asumehe na Igu.

Sauran sun Hada da,Alhaji Hassan Ibrahim,Ozauto of Igu Kingdom,Hon Alhassan Momoh,Boruwa ,Malam Muhammed Isah da Ramat,Uwhene OGBANI na sarautan Igu .

Da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da rawani, Ohimegye na koton karfe, Dokta Sai’du Akawu Salihu, ya ce an ba su mukaman ne saboda irin rawar da suke takawa wajen inganta manufofin masarautar Igu tsawon shekaru.

See also  Gwamna Ododo ya amince, ya amince a gyara tsoffin ayyukan ruwan Lakwaja – Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Kogi

A cewarsa, fitattun mutane 25 sun nuna kimarsu wajen bayar da gudummawar kason su don ci gaban yankinsa a fagagen ayyukansu na dan Adam a lokacin da aka fi bukatar irin wannan gudunmawa.

Ya yi nuni da cewa majalisar gargajiya ta masarautar Igu a karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da baiwa wadanda suka dace, inda ya jaddada cewa bayar da mukaman zai zama abin karfafa gwiwa ga masu son yin koyi da su.

Ya shawarci wadanda aka nada da su ci gaba da baiwa majalisa da gwamnati shawarwari masu ma’ana kan al’amuran da suka shafi rayuwar al’ummar jihar musamman ma kasa baki daya.

See also  Kungiyar Yan Jaridu ta Kogi ta zabi Zakari Abubakar-Ola a matsayin lambar yabo ta Mai Tallafawa Al'uma

Bikin wanda ya gudana a wurin Ohimegye ya samu halartar mai martaba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir, wanda ya yi sallar Juma’a a koton karfe, Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt Hon Aliyu Umar Yusuf, kwamishinan a bangaren albarkatun ma’adinai, Injiniya Abubakar Bashir Gegu, sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa na daga cikin mutanen da suka halarci bikin.

Visited 55 times, 1 visit(s) today
Share Now