Barr. Muhammad ya karrama mahaifiyar marigayiya

Yayin Da Yan uwa Suka Shirya Addu’ar Fida’u Ga Marigayi Hajiya Uwa

Daga Wakilinmu

Unguwan Kura da ke karamar hukumar Lakwaja, a ranar Lahadin ni ya cika makil a yayin da lauyoyi, alkalai, Khadisu da ma’aikatan shari’a na jihar Kogi suka halarci addu’ar Fidau ta kwana bakwai ga mahaifiyar Barr Usman Muhammad, darakta a ma’aikatar shari’a ta jihar Kogi.

Babban Limamin Masallacin Lakwaja, Sheikh Muhammad Aminu Shaban ya jagoranci wasu malaman addinin Musulunci da suka hada da , Babban Limamin Masallacin juma’a Unguwan Kura, Sheikh Abubakar Adamu, ya jagoranci addu’a fidau wadda ta gudana a Masallacin Dan Kano, Unguwan Kura, Lakwaja.

A wata hira da manema labarai a karshen addu’ar, Barr. Usman Muhammad wanda ya yi magana a madadin ‘yan uwa ya ce marigayiyar uwa ce saliha wacce rayuwarta ta sadaukar da kai ga Allah da yi wa bil’adama hidima, don haka ya yi addu’ar Allah ya karba mata a aljanna.

See also  FG orders suspension of adjusted electricity tariff

A cewarsa, “mahaifiyata ta kasance babbar mace da ta tsaya kan gaskiya da rikon amana. Ta rene mu da tsoron Allah kuma ta kasance mai kyautatawa da yarda da kowa ba tare da la’akari da inda kuka fito ba. Lallai ta bar gado mai girma. Allah yasa ranta ya huta”, yayi addu’a.

Ya kuma bayyana rasuwar mahaifiyarta a matsayin babu makawa, sannan ya bukaci masu imani da su yi imani da ranar karshe, ya bukaci musulmi da su yi koyi da Hajiya Uwa, wadda ya ce mace ce ta gari.

Daga cikin mutanen da suka halarci taron akwai: Shugaban jam’iyyar APC na Lokoja, Hon. Maikudi Bature, lauyoyi da alkalai da dama daga manyan kotunan taraya da na jujohi.

Visited 30 times, 1 visit(s) today
Share Now