Barr Ahmed yayi kira da a hada kai a tsakanin musulmi, yayin da suke gudanar da bukukuwan Edil-fitir

Daga Musa Tanimu Nasidi

Dan Darman Lakwaja, Barr Nasir Ahmed, ya yi kira hadin kai da fahimta
tsakanin musulmin kasar.

Ahmed, wanda kuma babban kansila ne a Masarautar Lakwaja, ya yi wannan kiran ne a sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi ta hanyar wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya bayyana wa manema labarai a Lakwaja ranar Laraba.

Ya yi nuni da cewa, zaman lafiya ya zama dole domin ci gaban kasar nan cikin sauri, masarautar Lakwaja da jihar Kogi baki daya.

Ya ce idan babu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma, ba za a samu ci gaba mai ma’ana ba.

See also  ‘Mu yi Koyi da tafarkin gaskiya’ Ola ya bukaci Musulmai a sakon Eid-el-Fitr

Dan Darman Lakwajan ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Maigarin Lakwaja, mai Martaba Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, a matsayin mai kula da zaman lafiya da al’ada, ba zai yi kasa a gwiwa ba a kokarinsa na hada kan al’ummar masarautar Lakwaja ta hanyar daukaka martabar al’umma.

Ya taya Maigari Lakwaja da ’yan uwa masu rike da sarautar gargajiya na masarautar Lakwaja murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara.

Visited 3 times, 1 visit(s) today
Share Now