Daga Musa Tanimu Nasidi
A ranar Alhamis 22 ga watan Maris 2024 ne aka shirya gudanar da Addu’ar Fidau ga Marigayi .Alhaji Iliyasu Waziri.
A wata sanarwa da ‘yan uwa suka fitar sun ce addu’ar wadda babban limamin Lakwaja, Sheikh Muhammad Aminu Sha’aban zai jagoranta za ta gudana ne a masallacin Alhaji Ahmadu .Bakason Matsi dake unguwan karaworo,,da misalin karfe 10 na safe.
Waziri ya rasu ne a ranar Talata a cibiyar kula da lafiya ta tarayya Lakwaja, bayan gajeriyar jinya da yi, an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Allah ya gafarta masa dukkan kurakuran sa, ya baiwa iyalai da al’ummar musulmi kwarin gwuiwar daukar batattu da ba za a iya maye gurbinsa ba, Amin.
Visited 21 times, 1 visit(s) today