
Ta’addanci: Gwamnatin Taraya tana tuhumar shugaban Miyetti Allah Bodejo
Daga Wakilin mu Gwamnatin tarayya tana tuhumar shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo kan kafa wata kungiyar ‘yan bindiga da aka fi sani da Kungiya Zaman Lafiya ba tare da izini ba. Shugaban da ake tsare da shi wanda ya kamata ya gurfana a gaban kotu ranar Laraba bisa umarnin kotun bai halarta…