Majalisar malamai ta Kogi ta raba Sama Da Naira miliyan Uku Ga Masu Karamin Karfi Su 63

••• gov Ododo ya bada tallafin N1m ga kwamitin zakka

Daga Musa Tanimu Nasidi

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya baiwa kwamitin zakka na jihar tallafin kudi N1m.

Ododo ya bayar da tallafin ne a wajen rabon kudaden zakka na sama da Naira miliyan uku ga matalauta 63 a fadin kananan hukumomi 21 a duk shekara a Lakwaja.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan albarkatun ruwa,Injiniya Muhammad Danladi Yahaya Farouk ya yabawa majalisar malamai ta jiha bisa yadda take rabawa masu marayu da musu Karamin Karfi a duk shekara.

Ya bayyana zakka a matsayin tsarin Musulunci da aka kafa domin rage wahalhalun da zawarawa da marayu da marasa galihu ke addabar al’umma tare da alkawarin yin hadin gwiwa da dukkanin kungiyoyin addinai a jihar.

See also  Dino Melaye zai farfado da kamfanin karafa na Ajaokuta idan ya zama gwamnan jihar Kogi

Tun da farko a jawabinsa na maraba, shugaban kwamitin zakkah, Alhaji Sulaiman Baba Ali, wanda ya samu wakilcin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt. Hon. Ahmed Umar Imam ya shawarci al’ummar Musulmi da su rika fitar da zakka da sadaka ga marasa galihu a cikin al’umma.

Ya siffanta zakka a matsayin sadaka da take taimakawa wajen tsarkake dukiya, da kara albarka a rayuwa da samun lada mai yawa yana mai jaddada cewa harajin wajibi ne akan kowane musulmi da aka tsara domin taimakon talakawa da karfafawa al’umma.

Ya kuma yi kira ga malaman addinin Islama kan wajabta wa mabiyansu muhimmancin zakka musamman a hudubarsu na ranar Juma’a.

See also  CUSTECH Kidnapped Students:Seven Additional Students Rescued

Muhimman abubuwan da suka fi daukar hankali a bikin sun hada da: Bayar da tsabar kudi Naira 50,000 kowannensu ga mutane 63 da suka amfana a fadin kananan hukumomi 21.

Bikin na bana ya samu halartar Maimarba Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, wanda ya samu wakilcin Wazirin Lakwaja, Alhaji Abdulrahman Idris, babban limamin Lokoja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban, da na ankpa, tsohon Grand Khadi. na jihar Kogi, alkalai da malaman addinin musulunci da dama.

.

Visited 5 times, 1 visit(s) today
Share Now