Maigarin Lakwaja ya yabawa masu rike da sarautar Gargajiya, ya kuma yi kira da a hada kai Domin Cigaban Lakwajawa

Daga Lakwaja

Maigarin Lakwaja , Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V, ya yabawa ‘yan majalisar masu rike da sarautar gargajiyar a masautar Lakwaja bisa goyon bayan da suka ba shi kafin nadinsa a matsayin Maigarin Lakwaja.

Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin bude taron ‘yan majalisun masautar na farko a Lokoja ranar Asabar.

Ya Kira su da su bada gudun mawan su domin kawo hadin kai, zaman lafiya da kuma ci gaban masautar Lakwaja.

Mai Martaba sarkin ya ci gaba da cewa, duk da irin kalubalen da ake fuskanta a masarautan gargajiya, yana da kwarin gwiwar cewa da goyon bayansu da shawarwarin su masarautar Lakwaja za ta bun kasa.

Visited 32 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  Lauretta ga DSS: "Sama ba za ta fadi ba idan kun kama Peter Obi"