Gwamna Ododo Ya Bukaci Musulmi Da Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci gaban Kogi

Daga Musa Aliyu Nasidi

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya yi kira ga al’ummar musulmin jihar da su yi amfani da watan Ramadan mai zuwa wajen yi wa jihar Kogi addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

Ododo ya yi wannan kiran ne a wajen bude laccocin watan Ramadan na bana wanda majalisar malamai ta jiha ta shirya a Lakwaja, ranar Asabar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Anthoney Janar kuma kwamishinan shari’a, Muiz Yunus Abdullah ya gargadi musulmi da su yi sadaka ga mabukata.

Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su kara himma wajen yin addu’o’i ga duk wata munanan dabi’u a cikin watan Ramadan.

See also  Eid-el-fitr: Danlami Sule Greets Muslim Ummah

A cewar gwamnan, dole ne musulmi su yi amfani da wannan dama domin su kasance cikin wadanda suka samu sake haifuwar ruhi sannan kuma a zahiri sun canza su zuwa kyau da gogewa ta iyali, unguwanni, sauran al’umma da ofisoshin da suke mu’amala da su.”

Tun da farko a nasa jawabin, Maigarin Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir 1V, wanda ya samu wakilcin Hon. isah Tanimu Umar ya yabawa majalisar bisa kokarinsu na yada addinin musulunci.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su sadaukar da kansu ga tsoron Allah ta hanyar taimaka wa marsu rauni a cikin watan Ramadan da kuma bayansa.

Taron ya samu halatar shugaban kungiyar Jama’atul-Nasir Islam na jiha, Ambasada Usman Bello da limamai da malaman addinin musulunci da dama.

See also  Invitation! Invitation!! Invitation!!!

An gudanar da addu’o’i ga shugabanin jihar da ma kasa baki daya.

Visited 5 times, 1 visit(s) today
Share Now