Farouk,Khalifa,Hakimi,Shugaban APC Sun Halarci Daurin Auren Dan Siraj Fatiha.

Daga Musa Aliyu Nasidi

Dan tsohon shugaban karamar hukumar Lakwaja, Abdulsalam Siraj Yusuf Abdullah a ranar Juma’a ya daura aure da Binta Ahmed Datti.

Daurin auren Fatiha wanda ya gudana a masallacin Unguwan Kura dake Lakwaja, ya samu halartar mai girma kwamishinan albarkatun ruwa Injiniya Farouk Muhammad Danladi Yahaya.

Haka kuma akwai shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na karamar hukumar Lakwaja, Hon. Maikudi Bature,Hakimin Gundumar D,Isah Baba Nasidi, Shugaban Jama’atul Nasir Islam na jahar Kogi, Ambassador Usman Bello da khalifa Nurudeen Yusuf Abdullah.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da: abokai da abokan aikin Hon. Siraj Yusuf Abdullah, a fadin jihar.

See also  Gwamna Ododo ya rantsar da sabbin Alkalai 10 da aka nada

Injiniya Farouk a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya taya Hon.Siraj na daurin auren cikin nasara, yana addu’ar Allah ya albarkaci auren.

Kwamishina, Ya kuma gargadi Abdulsalam da Binta da su sanya Allah a gaba a lamarinsu, su gina aurensu akan amana da hakuri da mutunta juna tare da kasancewa da addu’a a koda yaushe.

Visited 8 times, 1 visit(s) today
Share Now