Allah Ya yiwa Iliyasu Waziri rasuwa

Daga Alfaki Muhammad Nasidi

Allah ya yi wa Alhaji Illiyasu Waziri, tsohon Manajan Kasuwanci na Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) Lakwaja rasuwa.

Waziri ya rasu a jiya, Litinin, a cibiyar lafiya ta tarayya dake Lakwaja, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Har ya zuwa rasuwarsa, dan majalisar zartarwa ne a majalisar malamai ta jihar Kogi, Kingmaker a majalisar gargajiya ta kakanda.

Za’a yi jana’izar shi a makabartar musulmi unguwan kura da safiyar yau.

Waziri ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya.

Allah ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa dukkan kurakuran sa, Ya kuma baiwa iyalansa da abokansa da al’ummar musulmi kwarin gwuiwa wajen jurewa batattu wadanda ba za su iya maye gurbinsa ba.
Ameen.

Visited 10 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  Sporadic shootings in Maiduguri as soldiers protest non-payment of allowances