Ba a yi zanga-zanga kan tsadar kayan abinci a Lakwaja ba, in ji shugaban karamar hukumar Lakwaja

Daga Musa Tanimu Nasidi

Shugaban riko na karamar hukumar Lakwaja, Kwamred Abdullahi Adamu, a wata zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, ya bayyana cewa babu wani abu kamar zanga-zanga da Yan kasuwa Zika yi a Lakwaja, jihar Kogi, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka wallafa, ba THEANALYSTNG ba.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa abin da ya faru shi ne ‘yan kasuwar sun yi mubaya’a ga sabon Maigari na Lakwaja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi 1V wanda aka nada a matsayin Maigarin Lakwaja Bakwai kwanan nan.

A cewarsa: “Al’adarmu ce ‘yan kasuwa sukan rika baje kolin kayayyakin abinci ko kayan abinci a duk lokacin da za su ziyarci fadar a rukuni-rukuni, ‘yan kasuwar da aka kama a cikin labarin suna rike da doya da sauran kayan abinci, ‘yan kasuwa ne da suka ziyarci mai Martaba Sarkin Lakwaja, ba masu zanga-zanga ba ne. Adamu yace.

Visited 5 times, 1 visit(s) today
Share Now
See also  Ohimegye Igu Koton-Karfe Ya Kai Ziyara Ta'aziyya Ga Iyalan Marigayi Imam Abubakar Umar Gegu