Daga Musa Muhammad nasiy
An yi kira ga al’ummar Gundumar Mazabar” D” da ke karamar hukumar Lakwaja da su rungumi zaman lafiya da hadin kai domin samar da zaman lafiya da ci gaban yankin.
Shugaban wata kungiyar matsawa ‘yan siyasa, Ward D -G17, Alhaji Hassan Inuwa Manaja ne ya yi kiran a yayin wani taron tattaunawa da kungiyar ta shirya a Lakwaja ranar Asabar, inda ya jaddada cewa: “Ta hanyar hadin kai da tattaunawa ne kawai za mu iya mu shawo kan matsalolin dake hana mu ci gaban al’umma.
“Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki su samar da yanayi na mutunta juna, fahimtar juna, da juriya.
Ya zama wajibi a kan kowannenmu mu guji yin kalaman raba kan jama’a, mu inganta hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu.” manaja Yace.
Hassan ya ci gaba da cewa a matsayinsu na ‘yan kasa masu kishin kasa, gundumar D -G17 ta ci gaba da jajircewa wajen sake farfado da al’umma ta hanyar fadakar da jama’a mai inganci da nufin samar da canji mai kyau.
A nasa jawabin, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt.Hon. Umar Imam ya shawarci ‘yan siyasar yankin da su hada kai.
“Dole ne a daina kalaman batanci daga mutanen da ya kamata su misalta matsayi mafi girma. Yana da matukar muhimmanci in so in yi amfani da wannan kafar in kira shugabanninmu, ’yan siyasa da mabiyansu su rungumi hadin kai, da zaman lafiya.
Ya zama wajibi mu rungumi hadin kai da ci gaba a matsayin jagororin tafiyarmu baki daya.” Inji shi.
Wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da: Hon Suleiman Babadoko , Injiniya Yahaya Muhammad Danladi Farouk, Injiniya Sagir Abdulsalam da Dr Abubakar Yusuf Abdullah, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lakwaja, Hon Maikudi Bature da dai sauransu.